Nijar ta haramta fitar da kayan hatsi daga kasar

Matakin hana fitar da kayan abinci daga kasar zuwa wasu kasashen bai shafi makwaftanta, Bukina Faso da kuma Mali ba. A cikin sanarwar da aka fitar, ta ce Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar, Abdourahamane Tiani ya dauki matakin ne domin kare kayan abincin da ke a kasuwannin cikin gida tare da tabbatar da wadatarsu ga jama'a.

Karin bayani: Rage farashin kayan masarufi a Nijar

Sanarwra ta kara da cewa, duk wanda ya sabawa dokar zai fuskanci hukuncin dauri bayan an kwace kayansa. A gefe guda, ministan ayyukan noma na kasar, ya sha alwashin siyan wasu daga cikin kayan amfanin gona manoma, domin cike rumbunan abincin kasar. Nijar na kasancewa babbar mai shigar da kayan hatsi a wasu sassan Najeriya.

 


News Source:   DW (dw.com)