Nijar ta cimma yarjejeniya da Starlink don inganta intanet

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kulla yarjejeniya da hamshakin attajirin nan na Amurka Elon Musk mai kanfanin Starlink, domin inganta harkokin sadarwa na intanet a kasar. Gidan talabijinTélé Sahel da ya shelanta labarin, bai fayyace ka'idojin yarjejeniyar ba, amma ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani na Jamhuriyar Nijar, Sidi Mohamed Raliou, ya ce Starlink zai wadata kusan kashi 80% zuwa 100%" na Nijar da intanet mai inganci, kuma a farashi mai rahusa. A yanzu dai kashi 32% na kasar Nijar ne ke samun intanet, duk da kanfanoni hudu da ake da su da ke gudanar da wannan aiki.

 Wannan rattaba hannu da Starlink ya yi da Nijar ya tabbatar da ci-gaban da yake samu a yammacin Afirka, inda a ranar 11 ga watan Oktoba, Laberiya ta sanar da kulla irin wannan yarjejeniya ta samar da intanet da shi. Ita ma gwamnatin mulkin soja a Mali ta dage haramcin da ta kakaba wa Starlink na tsawon watanni shida. Amma dai, kamfanin Starlink yana ci gaba da fuskantar haramci a kasashe da dama na yankin, musamman Burkina Faso da C°ote d' Ivoire.


News Source:   DW (dw.com)