Nijar na shagulgulan karamar sallah

Nijar na shagulgulan karamar sallah
Nijar na gudanar da shagulgulan karamar sallar a yayin da makwabciyarta Najeriya ke azumi a wannan Lahadi biyo bayan rashin ganin jaririn watan Shawwal, da ake yin karamar sallah a cikinsa a yammacin ranar Asabar.

A Jamhuriyar Nijar a wannan Lahadi ne al'ummar Musulmin kasar ke gudanar da shagulgulan karamar sallah ko sallar azumi ta bana. Gwamnatin kasar ta bayar da umurnin gudanar da sallar a wannan rana bayan da hukumar koli ta harkokin addinin Muslunci ta kasar, Conseil islamique, ta sanar da ganin jinjirin watan Shawal a garuruwa akalla biyar na kasar a yammacin ranar Asabar.

Wakilin DW a Yamai Gazali Abdou Tasawa ya ce '' kusan gaba daya Musulimin kasar suka yi bikin sallar a wannan Lahadi.''

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar sun halarci sallar Idin a Yamai, suna masu isar da sako na zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.


News Source:   DW (dw.com)