Matakin na zuwa ne bayan da gwamnatin ta sanar da tsauraran manufofi kan shige da fice.
A wani sako da ta wallafa a shafin sada zumunta na X Ministar kula da neman mafaka da kaurar jama'a Marjolein Faber ta ce ta sanar da hukumar tarayyar Turai cewa kasar Netherlands na bukatar janyewa daga batutuwan da suka shafi kaurar jama'a.
Ta ce za su aiwatar da nasu tsarin na manufofin neman mafaka.
Kafin kasar ta Netherlands ta iya fita daga yarjejeniyar baki daya sai ta sami amincewar dukkan mambobin kasashe 27 na kungiyar tarayyar Turai EU.