Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya isa birnin Washington na Amurka domin tattaunawa a wanan Litinin kan mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza kafin daga bisani ya yi ganawar keke da keke a gobe Talata da Shugaba Donald Trump.
Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da aka bude sabon babin tattaunawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wanda zai ba da dama sakin rukunin mutane na karshe da Hamas ta yi garkuwa da su bayan harin ranar bakwai ga watan Oktoban 2023.
Karin bayani: 'Lokaci ya yi da za a tsara makomar Gaza'
Tun da farko dai Trump ya ba da shawarar kwashe Falasdinawa domin mayar da su zuwa wurare masu aminci kamar Masar da Jordan don tsaftace zirin Gaza lamarin da ya haifar da cece-kuce a fadin duniya.
A jiya Lahadi ne mista Netanyahu ya isa Amurka inda zai kasance jagoran kasar waje na farko da zai gana da Donald Trump tun bayan da ya karbi madafun iko, lamarin da ke nuna kyakkyawar dangantaka tsakanin Amurka da Isra'ila.