Netanyahu zai gana da Trump kan Gaza

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu zai kasance shugaba na farko daga kasar waje da zai ziyarci fadar White House tun bayan sake dawowar Donald Trump a kan karagar mulki.

Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna halin da ake ciki na tsagaita wuta tsakanin Israila da Hamas a Gaza tare da duba yiwuwar kawo karshen rikicin baki daya.

Kafin saukar sa a Amurka, ofishin Netanyahu ya sanar da cewa zai tura tawaga domin shiga tattaunawa a zagaye na gaba na Doha kasar Qatar da za a yi nan gaba a cikin wannan makon.

Sanarwar na zuwa ne yayin da Hamas ta tabbatar da kudirinta na shiga shawarwarin da Amurka da Masar da Masar da kuma Qatar suke shiga tsakani don samun masalaha.

Zagaye na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar za ta bayar da damar sako dukkan ragowar 'yan Israila da Hamas ta ke garkuwa da su da kuma cimma wata yarjejeniyar ta kawo karshen rikicin da ya faro a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Harin na Hamas kan Israila ya hallaka mutane 1,200 tare da yin garkuwa da wasu mutanen kusan 250

 


News Source:   DW (dw.com)