Kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya ICC ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministansa na tsaro Yoav Gallant da wani babban Jami'in mayakan Hamas Mohammed Deif bisa zargin laifukan yaki da laifukan keta haddin al'umma.
Matakin na ba zata ya janyo kakkausar martani daga Netanyahu wanda a cikin wata sanarwa ya ce Israila ta yi watsi da sammacin da zarge zargen da aka yi mata.
Kotun kasa da kasa ta ICC a HagueHoto: Reuters/E. PlevierKarin Bayani:ICC ta ce toshe agajin Gaza laifin yaki ne
Matakin na ICC dai a yanzu yana nufin zai takaita zirga zirgar Netanyahu da Yoav Gallant kasancewa kowace daga cikin kasashe 124 mambobin kotun na iya kama shi kan laifukan keta haddin al'umma da laifukan yaki da aka aikata daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa akalla ranar 20 ga watan Mayu 2024, ranar da mai gabatar da kara ya mika bukatar sammacin kamen.
Netanjahu tare da rakiyar sojoji a zirin GazaHoto: Maayan Toaf/Israel Gpo/ZUMAPRESS.com/picture allianceKarin Bayani: Matsayar Jamus kan bukatar kama Netanyahu
Haka kuma kotun ta bayar da sammacin kama babban Jami'i a kungiyar mayakan Hamas Mohammed Deif wanda Israila ta yi ikrarin cewa ta kashe a wani hari ta sama a kudancin Gaza a cikin watan Yuli, amma Hamas ba ta tabbatar da mutuwarsa ba.
Hamas ta ce ta yi maraba da matakin, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su bai wa kotun hadin kai don gurfanar da Netanyahu da Gallant su kuma hada hannu wajen dakatar da kisan kiyashi a kan fararen hula a zirin Gaza.