Netanyahu ya ce masu dasawa da Iran sun yi kokarin kashe shi

Firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kungiyoyin da Iran ke mara wa baya sun yunkurin kashe shi da mai dakinsa, bayan da ofishinsa ya sanar cewar wani jirgin mara matuki ya kai hari a gidansa da ke Caesarea. Sai dai Netanyahu wanda ofishinsa ya ce, ba ya gida a lokacin da lamarin ya faru, ya danganta wannan mataki da babban kuskure. Kuma a cikin sanarwar da ya fitar, ya mika sako ga Iran da wadanda suke dasawa da ita cewa, za su yi nadamar daukar wannan mataki, domin ba wanda zai cutar da 'yan kasar Isra’ila kuma ya kwana lafiya.

Karin bayani: Netanyahu ya yi barazanar lalata Lebanon saboda Hezbollah

Ya zuwa yanzu dai, Iran ba ta ce uffan ba game da wannan zargi. Amma ministan harkokin wajen Isra'ila Katz ya ce yunkurin kashe Netanyahu ya nuna ainihin fuskar Iran a idanun duniya. Dama arewacin Isra'ila ya fuskanci hari rokoki 115 da aka harba daga Lebanon, inda kungiyar Hezbollah ta daukin alhakin wadanda aka kai a Haifa da Safed. Sa dai gwamnati Isra'ila na ci gaba da shan alwashin samun nasara a  yakin da take yi da Hamas.


News Source:   DW (dw.com)