Neman gafara kan kisan Lumumba

Neman gafara kan kisan Lumumba
Tun bayan kisan fitaccen dan fafutikar 'yancin kan Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwango Patrice Lumumba, a karon farko a mikawa iyalansa hakorinsa da aka cire.

Firaministan Bejiyam Alexander De Croo ya sake rokon al'ummar jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango afuwa, game da batun kisan fitaccen dan fafutikar neman 'yancin kasar da yayi gwagwarmaya da Turawa 'yan mulkin mallaka Patrice Emery Lumumba da 'yan a birnin Katanga a shekarar 1961.

A gaban dandazon iyalan Lumumba a yayin wani bikin mika haurensa da 'yan mulkin mallakar Bejiyam suka cire bayan sun masa kisan gilla, Firaministan Bejiyam Alexander De Croo ya ce Bejiyam na cigaba da juyayin yadda aka kashe fitanccen dan fafutikar neman 'yancin, inda ya ce kasar ta da kuma dauki alhakin kisan.


News Source:   DW (dw.com)