Kungiyar tsaron ta NATO ta yi gargadin cewar za ta iya taimaka wa Ukraine idan har hakan ya cancanta, a nan gaba lokacin da kasar ta shiga cikin kungiyar EU. A halin da ake ciki Ukraine ta ce ta yi musayar sojoji fursunoni 144 da Rasha, ciki har da masu kare Azovstal 95 a Mariupol da ke kudu maso gabashin kasar, wadanda suka yi yaki a tashar jiragen ruwa da sojojin Rasha suka yi wa kawanya tsawon makonni kafin su mika wuya. Yawancin fursunonin da aka yi musayarsu sun ji munanan raunuka harsassai a cewar hukumomin na Ukraine. Kyiv da Moscow sun gudanar da musayar fursunoni da dama tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.