Najeriya za ta shiga cikin kungiyar BRICS

A cikin sanarwar da kasar Brazil da ke jagorantar kungiyar BRICS a bana ta fitar, ta yiwa Najeriyar maraba da kulla kawance da kungiyar da kasashen Rasha da Indiya da China suka kafa ta a shekarar 2009, inda a shekarar 2010, kasar Afirka ta Kudu ta shiga kungiyar. Sanarwar ta kara da cewa, a matsayinta ta shida mafi yawan al'umma a duniya kuma mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, kuma daya daga cikin kasashe mafiya karfin tattalin arziki a Afirka, Najeriya na da manufofin da suke kamanceceniya da sauran kasashe mambobin kungiyar ta BRICS.

Karin bayani: Putin ya karbi shugabanni a taron kolin BRICS

Gwamnatin Brazil ta ce Najeriya na kara karfafa alakarta da kasashen kudancin duniya da kuma sauya salon mulkinta, wanda hakan ke daga cikin manyan abun da gwamnatin Brazil mai ci ta sanya a gaba.

A shekarar 2024 ne kasashen Iran da Masar da Habasha da Hadaddiyar Daular Larabawa suka zama mambobi a BRICS. Kawo yanzu dai an mikawa Saudiyya goron gayyata cikin kungiyar, kana kungiyar ta bude wa wasu kasashen kofar shigowa.

 


News Source:   DW (dw.com)