Najeriya za ta kiyada al'umarta a badi

Najeriya za ta kiyada al'umarta a badi
Najeriya ta shirya aikin kididdige 'ya'yanta bayan tsawon lokaci ba tare da yin haka ba. Adadin 'yan kasar dai a yanzu sun zarta mutum miliyan 200 a cewar mahukunta.

Bayan kwashe shekaru 17 ba tare da lissafa yawan al'umarta ba, Najeriya ta ce za ta gudanar da aikin kidayar 'yan kasar a badi.

Bisa kiyasin mahukunta dai Najeriya a yanzu na da sama da mutum miliyan 200, kasar da ta fi yawan al'uma a nahiyar Afirka.

Kidayar jama'a dai batu ne da ke cike da rudani a kasar, saboda kishi na kabilanci da kuma kokari da kungiyoyin addinai ke yi wajen amfani da alkaluman don nuna karfinsu ta fuskar yawa.

Suna kuma nuna hakan ne musamman domin neman kaso mai tsoka daga arzikin kasa da ma iko na wakilci a siyasance.

Da ma a bara ne Najeriyar ta shirya aikin kidayar, amma aka dakatar saboda barazanar tsaro musamman sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa da ma hare-hare na 'yan bindiga.


News Source:   DW (dw.com)