Najeriya za ta fara rigakafin cutar kyandar biri ranar takwas ga watan Oktoban 2024 bayan hukumomi sun kammala amincewa da alluran da za a yi amfani da su.
Mai magana da yawun hukumar lafiya a matakin farko ta kasar ne ya tabbatar da ranar fara rigakafin ga manema labarai.
Najeriyar ta karbi kason farko na rigakafin kyandar biri dubu 10 daga kasar Amurka a ranar Talata.
Jamus za ta bai wa Afirka rigakafin cutar Kyandar Biri
Kasar ta kuma tabbatar da mutum 40 ne suka kamu da kyandar biri amma ba tare da samun mutuwa ba ya zuwa karshen mako.
Alluran rigakafin cutar kyandar biri guda 10,000 ne suka isa nahiyar Afirka, amma maimakon Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke zama tungar cutar ta fara cin gajiya, Najeriya ce ta kasance a sahun farko wajen samun su daga Amurka.
Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika
Ya zuwa yanzu kasar da ke yammacin Afirka ba ta samu mace-mace ba tun bayan bullar cutar a Najeriya.
Cutar ta kyandar biri dai ta fi kamarai ne a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango, sai dai kuma ta bazu zuwa wasu kasashen duniya.