Najeriya: Za a maido da shingen bincike

Najeriya: Za a maido da shingen bincike
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwar da ke bayyana bukatar tsaurara matakan tsaro a makarantu da asibitoci a daukacin kasar, a yayin da ake ci gaba da samun karuwar ayyukan ta'addanci.

Sanarwar da rundunar ta fidda a yau Lahadi, ta umurci maido shingen bincike da zai bayar da damar duba ababen hawa a lokacin da za su shiga gine-ginen gwamnati.

Sai dai shugaban 'yan sandan ya umurce su da yin aiki cikin kwarewa ba tare da cin zarafin 'yan kasa da ma amsar na goro ba. Wannan sabon matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar da ke da mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, ke shirye-shiryen tunkarar zaben gama gari a shekarar da ke tafe.

Al'umma a Najeriya da ma masu rajin kare su na martani a game da wannan mataki na maido da shingen bincike, wanda suka ce duk da alkawarin da mahukuntan kasar suka yi na maido da da'a a tsakanin jami'an 'yan sanda har yanzu suna ci gaba da tsohuwar dabi'arsu wacce a shekarar 2020 ta jefa kasar cikin hargitsi da ya yi sanadiyar rayukan mutane musamman ma a jihar Legas.


News Source:   DW (dw.com)