Mahara sun far wa kauyukan ne kan Babura inda suka dinga harbe mutane tare da kone gidaje. Wasu mazauna kauyukan da aka kai harin sun ce har zuwa yammacin jiya Lahadi suna kan kokarin gano gawawakin mutane da harin ya ritsa dasu a kauyukan Kukawa, da Gyambau da kuma Kyaram.
Wakilin mu na jihar Filato Abdullahi Maidawa Kurgwi, ya zanta da Alhaji Danjuma Sarkin Pawan Kukawa, wanda kuma ya bayyana masa cewa maharan sun kashe mutane da dama bayan da suka kai farmaki a garin na Kukawa inda suka kashe mutum 24.
Kokarin da wakilinmu na samun karin bayani daga hukumomin tsaro a jihar ta Filato ya ci tura, sai dai wata majiya ta ce an hango motocin jami'an tsaro a yammacin jiya lahadi suna kokarin shiga wuraren da aka kai hare-haren.