Najeriya ta bai wa Rwanda alluran rigakafin cutar kyandar biri

Kasar Rwanda ta kaddamar da aikin rigakafin cutar kyandar biri wato Mpox a fadin kasar, bayan samun allurori dubu daya daga Najeriya, bisa wata yarjejeniya da kasashen biyu suka cimma, kamar yadda hukumar kula da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka CDC ta sanar.

Karin bayani:An samar da makuden kudi na dakile cutar Mpox a Afirka

Za a gudanar da aikin rigakafin a yankuna bakwai na kasar, wadda ita ce cibiyar da cutar ta fi kamari a nahiyar Afirka, inda a makon da ya gabata kadai aka samu rahoton bullar cutar a kan mutane dubu biyu da dari tara da sha biyu, da mutuwar mutane 14.

Karin bayani:Cutar kyandar biri ta mpox ta halaka mutane a kasar Kamaru

Ya zuwa yanzu dai mutane 738 cutar ta halaka a Rwanda, bayan kamuwar mutane dubu shida da goma sha biyar, tun daga farkon wannan shekara zuwa yanzu.

Amurka ce dai ta bai wa Najeriya tallafin allurai dubu goma, kuma a ciki ne Najeriyar ta bai wa Rwanda dubu daya.


News Source:   DW (dw.com)