Najeriya: Saukaka hanyoyin samun bashi ga 'yan kasa

A Jawabin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na murnar shiga sabuwar shekarar 2025 ga 'yan kasar, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin tarayyar za ta samar da kamfanin samar da bashi ga 'yan kasar, tare da hadin gwiwa da bankin masana'antu da wasu hukumomin kudi har ma da ma'aikatun gwamnati, da nufin saukaka karbar bashi a kasar.

Ya kuma kara da cewa, wannan shirin zai kara inganta bangaren hada-hadar kudi da kara fadada hanyoyin samun bashi da kuma bayar da goyon baya ga bangarorin da ba a cika damuwa da su ba, kamar mata da matasa. Dama dai tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a shekarar 2023, Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin sake fasalin karbar bashi a kasar domin habaka tattalin arziki.

 


News Source:   DW (dw.com)