Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jinjina wa dakarun sojan kasar bisa kisan gawurtaccen dan bindigar nan Halilu Sububu wanda ya addabi jihohin Arewa maso gabashin kasar, da kuma wani fitaccen dan bindigar daji Sani Wala Burki da jami'an Najeriya suka yi ikrarin kashewa a Katsina.
Karin Bayani : Sabbin matakan tsaro a Jihar Sokoton Najeriya
Fitaccen dan bindigar da ya yi kaurin suna a jihohin Sokoto da Zamfara, ya gamu da ajalinsa ne a yayin wani dauki ba dadi da hadin gwiwar sojojin saman Najeriya da na kasa suka yi da 'yan bindigar ne a ranar Alhamis da ta gabata, inda sojojin suka tabbatar da hallaka shi tare da wasu manyan 'yan bindigan kusan mutum 40.
Jami'an tsaron Najeriya sun kwashe tsawon shekaru sun fama da wadannan gungun mutane da ke sace al'umma da karfin bindiga domin neman kudin fansa.
Karin Bayani : Gwamnatin Najeriya na shirin daukar mataki a kan 'yan bindigar daji
A yan kwanakin nan ne sojojin na Najeriya suka sha alwashin magance wannan matsa ta yan bindigar daji, inda har ma babban hafsan hafsoshin Najeriya ya tabbatar da yunkurinsa na kashe Bello Turji guda daga cikin manyan barayin dajin da suka yi fice a arewacin Najeriya.
Halilu Sububu wanda ya jima yana hakar ma'adanai ta barauniyar hanya da ma sayar da bindigogi ga yan bindigar ya addabi al'ummar jiharsa ta Zamfara da ma makwabtan jihohi kamar Sokoto da Katsina da Kaduna.