Galibin sassan Najeriya sun kwashe kwanaki uku ba tare da samun wutar lantarki ba, sakamakon lalata wasu layukan samar da wuta ta Odukpani Ikot Ekpene, da ke jihar Akwa Ibom a kudancin kasar.
Sau da dama ne dai cibiyar samar da wutar ta Najeriya ke lalacewa cikin wannan shekarar, kuma karo na biyu cikin wata guda da ya gabata.
Matsalar da ta kazanta daga ranar Juma'a, ta haddasa rashin akalla megawatt 400 da cibiyar ke iya samar wa sassan kasar da dama.
Yawan daukewar wutar lantarki dai wata babbar matsala ce da ta jima a kasar da ta fi yawan al'uma a nahiyar Afirka.
Sana'o'i da dama da suka dogara da wutar lantarki dai na durkushewa saboda dogaro da suke yi da injunan janareta da ke da matukar tsadar gudanarwa.