Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa wata babbar kotun kasar da ke zamanta a Yenagoa babban birnin jahar Bayelsa, ta yanke hukuncin da ke amince wa tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan tsayawa takara a zaben shekarar 2023 da kasar za ta yi.
Sai dai har ya zuwa wannan lokaci tsohon shugaban bai bayyana ko zai yi takara a zaben da ke tafe ba, a baya gamayyar kungiyoyin arewacin kasar sun saya mishi tikitin takara, amma kuma daga bisani ya nesanta kanshi da hakan.
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da al'umma a kasar ke bayyana shakku ko Mista Jonathan zai iya yin takara. A shekarar 2018 ne shugaban kasar Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a gyaran fuskar da aka yi wa dokar da ta takaita wa mataimakin shugaban kasa da ya maye gurbin shugaba ko dai ta hanyar mutuwa ko kuma a sabili da wani rashin lafiya na karasa wannan wa'adi da kuma yin wani wa'adi guda daya kacal, gyaran dokar da wannan kotun ta ce, bai shafi Ebele Jonathan ba.