Najeriya: Jiragen sama za su fasa aiki

Najeriya: Jiragen sama za su fasa aiki
Kamfanonin sufrin jiragen sama masu zaman kansu a Najeriya na shirin dakatar da zirga-zirgar jiragensu a wannan Litinin bisa tsadar farashin man jirgi na jet da ake fuskanta.

Matakin ya biyo bayan tashin farashin kudin litar man jirgi daga Naira 190 zuwa 700 a cewar kungiyar Airline Operators of Nigeria. Sai dai ma'aikatar harkokin sufrin Najeriya ta gargadi kamfanonin da su kiyaye illar da hakan ka iya haifar wa matafiya na ciki da na wajen Najeriya idan matakin ya soma aiki.

Yanzu hakan dai duniya na fuskantar tashin farashin kayayakin bukatu irin na yau da kullum ciki har da man jirgi, tun bayan da aka fara fafata yaki tsakanin Ukraine da  makwabciyarta Rasha makwanni da dama da suka gabata.

Duk da dumbin arzikin mai da Allah ya albarkaci Najeriyar da shi, kasar na ta'allaka da man da ake fito mata daga waje, lamarin da ke kara dagula wasu al'amurra na kasuwannin cikin gida, inda ko a baya bayan nan aka fuskanci katsewar wutar lantarki bisa karin farashin kudin mai.


News Source:   DW (dw.com)