Najeriya: Goodluck Jonathan zai iya yin takarar shugaban kasa

Najeriya: Goodluck Jonathan zai iya yin takarar shugaban kasa
Wata kotu a Najeriya ta ce tsohon shugaban kasar Goodluck Johnathan zai iya yin takara neman shugabancin kasar a zaben da ke tafe.

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa wata babbar kotun kasar da ke zamanta a Yanagoa baban birnin Bayelsa, ta yanke hukuncin da ke amincewa tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan tsayawa takara a zaben shekarar 2023 da kasar za ta yi. 

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da al'umma a kasar ke bayyana shaku ko Mista Johnathan zai iya yin takara ko kuma a a .

A shekarar 2018 ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a gyaran fuskar da aka yi wa dokar da ta takaita wa mataimakin shugaban kasa da ya maye gurbin shugaba ko dai ta hanyar mutuwa ko kuma a sabili da wani rashin lafiya na karasa wannan wa'adi da kuma yin wani wa'adi guda daya kacal, gyaran dokar da wannan kotun ta ce bai shafi Ebele Jonathan ba.

Sai dai har ya zuwa wannan lokaci tsohon shugaban bai bayyana ko zai yi takara a zaben da ke tafe ba, a baya gamayyar kungiyoyin arewacin kasar sun saya mishi tikitin takara, amma kuma daga bisani ya nesanta kanshi da hakan.
 


News Source:   DW (dw.com)