Rahoton hukumar ya kuma bayyana cewa tuni mutum daya ya mutu sanadiyar cutar. Tara daga cikin wadanda suka kamu da cutar mazauna birnin Abuja ne, da ke zama babban birnin kasar.
Hukumar ta ce tun a watan Janairun da ya gabata suka zargi cewa mutane 61 sun kamu da cutar. A Nahiyar Afirka, an fi samun bullar cutar ta kyandar biri a kasashen Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango da ma Najeriyar. A baya.-bayan nan cutar ta haifar da fargaba, inda aka tabbatar da fiye da mutane 200 sun kamu da ita a kasashe 19, wanda yawanci kasashen Turai ne.