Najeriya ta zama kasa ta farko a duniya da ta fara amfani da rigakafin R21 da masana kimiyya na jami'ar Oxford suka gano. Ministan lafiya na kasar, Muhammad Ali Pate ya ce Najeriya ta karbi rigakafin fiye da guda 846,000, ake kuma sa ran karbar sauran guda 154,000 nan da ranar 26 ga watan Octoban 2024.
Ministan ya bukaci 'yan Najeriya da su yi kokarin cin gajiyar wannan dama domin kare kawunansu daga cutar. Za a fara mika rigakafin ne ga jihohin Kebbi da kuma Bayelsa.
Karin bayani: Cutar maleriya na barazana a Afirka
Alkalumma Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da cewa, Najeriya ce kasa mafi fama da matsalar cutar Maleriya. Cutar na yin sanadin rayukan mutane dubu 600 a duk shekara wanda yawancinsu jarirai ne da yara da ke nahiyar Afirka.