Najeriya da Nijar sun kulla sabuwar yarjejeniyar tsaro

Kasashen Nijar da Najeriya sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar karfafa tsaro a tsakaninsu, a karon farko tun bayan dagulewar diflomasiyya a tsakaninsu lokacin da soja Janar Abdourahamane Tiani ya tunkude zababbiyar gwamnati a shekarar da ta gabata.

Wannan dai na zuwa bayan ganawar da hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Musa Christopher da takwaransa na kasar Nijar Birgediya Janar Moussa Salaou Barmo ya yi a birnin Yamai na Jamhuriyar ta Nijar a Larabar da ta gabata.

Gabannin zaman dai, kungiyar bunkasa kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, a karkashin Najeriya ta yi barazana afka wa sojojin Nijar domin tilasta wa masu juyin mulkin dawo da hambararren shugaba Mohamed Bazoum, matakin da ya fusata gwamnatin mulkin sojin Nijar, ta kai ga ficewa daga cikin kungiyar ECOWAS tare da kulla sabuwar alaka da kasashen Mali da Burkina Faso.

 


News Source:   DW (dw.com)