Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya furta cewa a ranar Juma'a yakin da kasarsa ke gwabzawa da Rasha zai kawo karshe nan ba da jimawa ba, idan zababben shugaban Amurka Donald Trump ya fara jan ragamar mulki.
Zelensky ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da kafafen yada labaran cikin gida na Ukraine, inda ya yaba tare da nuna gamsuwarsa kan canja yawun da suka yi a baya-bayan nan da Donald Trump duk da fargabar da yake yi ta raguwar tallafin da kasarsa ke samu daga Amurka. Shugaban na Ukraine ya ce 'na yi imanin cewa yakin da kasata ke yi da Rasha zai kawo karshe a karkashin manufofin sabuwar gwamnatin da za ta jagoranci Amurka' sai dai amma Zelenky bai fadi lokaci da yake tunanin yakin zai kare ba.
Karin bayani: Rasha ta musanta tattaunawar Putin da Trump a kan Ukraine
A lokacin yakin neman zabe dai Donald Trump ya yi alkawarin kawo karshen yakin Ukraine da Rasha a cikin sa'o'i 24 kacal, kuma ko da a ranar Juma'a shugaban mai jiran gado ya yi alkawarin yin aiki tukuru don bullo wa lamarin.