Mutuwar Carter: Amurka ta shirya jana'izar ban girma

Tuni dai aka yi kasa-kasa da tutocin kasar ta Amurka a dukkan hukumomi da ma'aikatun gwamnati da ke fadin kasar a matsayin makokin bankwana da gwani kuma shugaban kasar mafi dadewa Jimmy Carter wanda ya rasu a jiya Lahadi yana da shekaru 100.

Karin bayani:Tshohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya mutu yana da shekaru 100 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog da shugaban kasar China Xi Jinping na daga cikin shugabannin da suka nuna alhini na mutuwarta Carter. Daga can kuwa fadar Vatican, Fafaroma Francis ya bayyana marigayin a matsayin mai tsoron Allah da kuma kishin addini.

 


News Source:   DW (dw.com)