Mutun hudu sun mutu a Jamus bayan hari a kasuwar Kirisimeti

Jamus ta wayi gari cikin bacin rai da kuma alhini bayan harin da wani direba ya kai a lokacin da ya kutsa da mota cikin cunkoson jama'a a kasuwar Kirisimeti tana tsaka da ci a birnin Magdeburg da ke gabashin kasar a daren Juma'a.

Wannan lamari da ya ritsa da rayukan mutane hudu tare da jikkata wasu mutanen kusan 200 ciki har da wandanda suka ji munane raunuka ya fusata Jamus matuka har ma da wasu kasashe.

Tun a lokacin da lamnarin ya auku wani kwararren likita mai suna Taleb.A dan asalin kasar Saudiyya da ke zaman mafaka a Jamus kuma ma'aikaci a asibitin birnin Megdeburg mai suna Taleb.A da aka bayyana a matsayin maharin ya shiga hannun 'yan sanda.

Kasashe da dama sun yi tir da wannan hari da har kawo yanzu ba a hakikance musabbabinsa ba, sai dai amma jaridar Der Spiegel ta Jamus ta kawar da maganar harin ta'addanci yayin da wasu ke kusanta maharin da masu ra'ayin kyamar baki sannan wasu kuma ke cewa ba ya rasa damuwa a kwakwalwarsa.

A wannan Asabar Olaf Scholz zai kai ziyara birnin na Magdeburg domin nuna alhini kan wannan lamari da ya yi kama da wanda ya auku a birnin Berlin fadar gwamnati Jamus a shekarar 2016 a daidai wannan lokaci. 


News Source:   DW (dw.com)