Jamus ta wayi gari cikin bacin rai da kuma alhini bayan harin da wani dreba ya kai a lokacin da ya kutsa da mota cikin cunkoson jama'a a kasuwar Kirisimeti tana tsaka da ci a birnin Magdeburg da ke gabashin kasar a daren Juma'a.
Wannan lamari da ya ritsa da rayukan mutane biyu tare da jikkata wasu mutanen 60 ciki har da wandanda suka ji munane raunuka ya fusata Jamus matuka har ma da wasu kasasshe.
Tun a lokacin da lamnarin ya auku wani kwararren likita dan asalin kasar Saudiyya da ke samun mafaka a Jamus kuma ma'aikaci a asibintin birnin Megdeburg mai suna Taleb.A da aka bayyana a matsayin maharin ya shiga hannun 'yan sanda.
Kasashe da dama sun yi tir da wannan hari da har kawo yanzu ba a hakikance musababbinsa ba, sai dai amma jaridar Der Spiegel ta Jamus ta kawar da maganar harin ta'addanci yayin da wasu ke kusanta maharin da masu ra'ayin mazan jiya sannan wasu kuma ke cewa ba ya rasa damuwa a kwakwalwasa.
A wannan Asabar Olaf Scholz zai kai ziyara birnin Magdeburg domin nuna alhini kan wannan lamari da ya yi kama da wanda ya auku a birnin Berlin fadar gwamnati Jamus a shekarar 2016.