Mutum sama da 18 sun mutu a harin Amirka

Mutum sama da 18 sun mutu a harin Amirka
Wani dan bindiga mai shekaru 18 ne ya kai hari kan makarantar Firamaren da ke jahar Texas inda nan take ya kashe dalibai kimanin goma sha tara.

Yara masu kananan shekaru akalla goma sha tara aka tabbatar sun mutu a sakamakon harin da wani matashi ya kai kan wata makarantar firamare ta Robb Elementary da ke jahar Texas a yammacin jiya Talata. Gwamnan jahar Greg Abbot ya sheda cewa, jami'an 'yan sanda da suka yi kokarin dakatar da maharin a lokacin da ya bude wuta a kan daliban, sun bindige shi har lahira. Dan shekaru sha takwas a duniyan, ya soma da harbin kakarsa da yanzu haka ke cikin mawuyacin hali a asibiti kafin ya isa makarantar.

Shugaba Joe Biden da ke kamalla ziyararsa a yankin Asiya yayi wa 'yan kasar wani jawabi mai ratsa jiki kan dalilan da ke janyo ire-iren wadannan hare-haren. Harin na ranar Talata da ke zuwa makonni biyu da wani farar fata ya hallaka bakaken fata goma, ya kasance daya daga cikin munanan hare-haren da aka kai a wata makaranta a Amirka, tun bayan wanda aka kai da ya salwantar da rayuka kimanin ashirin da takwas a Sandy Hook da ke jihar Connecticut kusan shekaru goma da suka gabata.


News Source:   DW (dw.com)