Mutum 80 sun tsallake rijiya da baya a hadarin jirgin Canada

Mai rikon mukamin Magajin Garin birnin Toronto Olivia Chow ta ce ta yi matukar kaduwa da jin labarin afkuwar lamarin, duk da cewa ta samu nutsuwa bayan jin cewa ba a samu asarar rayuka ko da guda daya ba daga cikin fasinjoji da ma'aikatan jirgin su kimanin 80, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

Karin bayani: Jirgin fasinja ya yi karo da na soji a Amurka

Hadarin jirgin na Toronto na zuwa a 'yan kwanaki da samun hadararrukan jiragen sama a arewacin Amurka da suka hada da taho mu gaba da wani jirgin helikwafta na soji ya yi da wani jirgin fasinja a birnin Washington wanda ya halaka mutane 67, da kuma wani hadarin jirgin daukar marasa lafiya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai a Philadelphia, sai kuma wani hadarin jirgin da ya halaka mutane 10 a Alaska.

 


News Source:   DW (dw.com)