Mutum 48 sun mutu sakamakon ruftawar mahakar zinare a Mali

Akalla mutane 48 sun mutu a yammacin Mali a jiya Asabar samakakon ruftawar rami a wani guri da ake hakar zinare ba bisa ka'ida ba kamar yadda majiyoyin 'yan sandan kasar da ta yi kaurin suna wajen samun aukuwar irin wadannan hadura suka tabbatar.

Lamarin da auku a tsohuwar mahakar ma'adinai ta garin Bilaly Koto inda wani kamfanin China ya yi aiki a shekarun baya, kuma galibin wadanda suka mutu mata ne matasa ciki har wata da ke dauke da goyon karamin yaro.

Mahukuntan yankin da lamarin ya auku sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike wakila za a samu karin wasu mutanen da kasa ta binne ramin da su.

An dai cika samun irin wadannan hadura a Mali a guraren hakar zinari na bayan fage, na baya-bayan nan ma shine wanda ya auku a kudancin kasar inda rayukan mutane sama da 15 suka salwanta.


News Source:   DW (dw.com)