Hukumomi a gabashin Indiya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 46 sakamakon nutsewa a ruwa yayin wani bikin mabiya addinin Hindu.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce mutanen sun rasu ne a wurare daban-daban a jihar Bihar a yayin da suka je wankan tsarki a kogunan da suka cika kuma suka tumbatsa.
Karin bayani: Gobara ta halaka mutane da dama a Indiya
Daya daga cikin jami'an hukumar da bai sahale a ambaci sunansa ba ya ce mutane sun yi biris da gargadin hukumomi na hadarin da ke tattare da shiga kogunan a yayin da ambaliya ta ke ganiyarta a damunar bana.
Tun a ranar Talata ne aka fara samun labarin nutsewar mutanen a yankuna 15 na jihar ta Bihar a yayin da ake bikin Jitiya Parv Hindu na mabiya addinin Hindu da uwaye ke yi don sama wa 'ya'yansu lafiya da kuma tsarki.
Karin bayani:Mata a Indiya na zanga-zanga kan halaka wata likita
Gwamnatin jihar ta ce za ta biya diyya ga iyalan mamatan 46 da suka gamu da wannan iftila'in yayin wankan tsarkin addininsu.