Mayakan 'yan tawayen kungiyar M23 sun jaddada cewa garin Goma mai tasiri na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na hannunsu, mai iyaka da kasar Ruwanda. Sai dai har yanzu babu wata sanarwar game da halin da ake ciki daga mahukuntan birnin Kinshasa fadar gwamnatin kasar.
Ana zargin kasar Ruwanda da taimakon 'yan tawayen wadanda suka hargitsa lamura a yankin na gabashin Kwango, inda cikin mako guda na rikicin ya raba kimanin mutane dubu-400 da gidajensu.
Karin Bayani: Rikicin Jamhuriyar Kwango da Ruwanda ya yi kamari
Rikicin garin garin Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: AFP TV/AFP/Getty ImagesShugaba Felix Tshisekedi na kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya tattauna ta wayar tarho tare da sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Marco Rubio wanda ya yi tir da tashin hankalin da ke faruwa a garin Goma. Sannan Rubio ya nuna takaicin yadda gwamnatin Ruwanda ke goyon bayan 'yan tawayen inda ya jaddada matakin mutunta 'yancin kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya tattauna ta wayar tarho tare da Shugaba Paul Kagame na Ruwanda game da tashe-tashen hankula da ke kara ta'azzara a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.
Ofishin shugaban na Afirka ta Kudu ya ce shugabannin biyu sun bayyana bukatar ganin samun yarjejeniyar tsagaita wuta, da komawa tattaunawa tsakanin bangarorin da ke rikicin.