Hukumar ta ce wannan adadi abun tayar da hankali ne kasancewar wannan ne karon farko da aka taba samun alkaluma mai yawa a tarihi.
Alkalumman hukumar a bara sun yi nuni da cewa kimanin mutane miliyan 90 ne suka rasa matsagunnansu biyo bayan rikice-rikice a kasashen Habasha da Burkina Faso da Myanmar da Najeriya da Afghanistan da kuma Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango.
Mamayar da Rasha ta kaddamar a kasar Ukraine a watan Fabarairun wannan shekarar kuma ya haifar wa mutane fiye da milyan takwas rasa matsugansu yayin da wasu kimanin miliyan shida suke gudu daga kasar kwata-kwata.