Mutun daya ne kadai ya tsira daga hadarin faduwar jirgin sama da ke jigilar mutane, wanda ke dauke da fasinja 21 a cewar ministan harkokin yada labaran kasar da yake tattaunawa da kamfanin dillancin yada labarai na Franasa.
Karin bayani: Sudan ta Kudu ta kafa dokar hana fita bayan zanga-zanga
Rahotanni sun ce jirgin da ke jigilar jama'a daga Juba babban birni, zuwa kudancin kasar ya fadi ne a tazarar kilo mita 500, jim kadan bayan da ya tashi daga filin jirgi.
Babu wasu takamaiman rahotannin da suka tabbatar da dalilin hadarin, amma kuma ma'aikatar cikin gidan Sudan ta Kudu, ta sanar da yunkurinta na gudanar da bincike kan musabbabin iftila'in.
Karin bayani: Kungiyar MSF ta ce 'yan gudun hijra na kwararra Sudan ta Kudu
A shekarar 2021 wasu mutane biyar sun ce ga garinku, bayan faduwar wani jirgin dakon man fetur mallakar hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.