Ministan Sufuri na Koriya ta Kudu ya ce kamanin mutane 120 suka mutu kamar yadda jami'an hukumar kashe gobara suka bayyana duk da cewa adadin ka iya zarta hakan. Kafofin yada labaran kasar sun ce jirgin ya fuskanci matsalar birki gabanin ya kammala sauka wanda daga bisani ya daki katangar wani gini inda jirgin ya kama da wuta.
Karin bayani: Jirgin sama ya kama da wuta bayan hadari a Tokyo na Japan
Wannan ne karon farko da jirgin na kamfanin Jeju Air ya yi hadari tun bayan assasa kamfanin a shekara ta 2005, wanda kuma ke jigilar matsakaitan fasinjoji.
Hadarin jirgin na zuwa ne kwanaki da wani makamancinsa da ya faru da wani jirgin saman Azerbaijan, da ya janyo asarar rayuka.