Wasu sabbin hare-hare da 'yan tawayen ADF da ke da alaka da kungiyar IS suka kai a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 12. Hukumomin yankin sun bayyana cewa, an kai hare-haren ne a daren Laraba, inda suka kashe mutane takwas a kauyen Bilendu, sannan suka kashe wasu karin mutane hudu a kauyen Mangoya, yayin da a daya hannun kuma maharan suka kona gidaje a kauyukan biyu.
Karin bayani: Kwango: Sabon rikici a arewacin Kivu
Dama dai, wadannan 'yan bindiga na ADF, wadanda akasarinsu Musulmi ne daga Yuganda, sun saba kashe dubban fararen hula tare da kwasar ganima a yankin Arewa maso gabashin Kwango, duk da tura sojojin Yuganda da na Kwango domin yakar su. Wannan yankin na gabashin Kwango ya fara samun kwanciyar hankali tsakanin watan Agusta zuwa Nuwamban 2024. Amma a lokacin bukukuwan Kisrimeti, 'yan tawayen ADF sun kai hare-hare inda suka kashe mutane 21 a lardin Kivu ta Arewa. Tun a shekarar 2019 ne, kungiyar 'yan tawayen ADF ta ayyana mubaya'a ga kungiyar IS.