Saudiyya ta ce za ta bai wa Musulmi miliyan guda daga ciki da ma wajen kasar damar aikin Hajji a bana, damar da ake gani ta farko tun bayan bazuwar annobar corona a duniya.
Sai dai hukumomin kasar sun ce wadanda za su yi aikin Hajjin da za a yi cikin watan Yuli a banan, dole ne su kasance 'yan kasa da shekaru 65 da haihuwa, kuma sun samu cikakkun alluran rigakafin corona.
Shekaru biyun da suka gabata ne dai aka yi matukar rage adadin mahajjata saboda gudun barazanar coronar.
A baya dai Musulmi akalla miliyan biyu da dubu 500 ne ke aikin na Hajji daga ko'ina a duniya, daya daga cikin shika-shikan addinin Islama.
Ana dai kwadaita wa Musulmi baligi da ke da karfi da cikakkiyar lafiya, da ya yi aikin na Hajji akalla sau guda a rayuwarsa.