Guguwa mai karfin gaske na ci gaba da rura wutar dajin da ta kama a garuruwa da ke kusa da birnin Los Angeles na Amurka a ranar Laraba.
Lamarin ya tilasta wa dubban mutane tserewa daga gidajensu ciki har da wadanda ke rayuwa a saman tsaunuka na kasaita.
Gobarar daji ta halaka mutane a Chile
Guguwar ta kuma rika kawo cikas ga aikin kashegobara a tsaunukan Santa Monica da Malibu wurare da suka kasance matattarar 'yan fina-finan Hollywood da mawaka da sauransu.
Wasu daga cikin taurarin shirya fina-finan Hollywood da lamarin ya shafa sun rika wallafa hotuna da bidiyon motocin nasu a kafafen sada zumunta tare da nuna alhini kan abinda ke faruwa.
Masu aikin kashe gobara sun rika amfani da motocin gireda wajen ture motocin hawa masu tsada a kokarin kawar da su daga inda gobarar ta dosa.
Gobara ta kone masana'antar kera makaman Turkiyya
Akwai masu aikin kashe gobara sama da 1,400 a bakin aiki sannan wasu daruruwan na kan hanya kamar yadda gwamnan jihar California Gavin Newsom ya fada wa manema labarai.