Muhawara a MDD kan kasar Rasha

Muhawara a MDD kan kasar Rasha
Kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya G7 ta yi kiran a dakatar da Rasha daga wakilci a hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Dunuiya sakamakon ta'asar da ta tafka a Ukraine.

Ministocin harkokin waje na kasashen Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Birtaniya da kuma Amirka suka gabatar da bukatar a cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan Alhamis.

Nan gaba babban zauren Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'ar dakatar da Rasha daga hukumar ta kare hakkin dan Adam bayan zargin kisan fararen hula da Rasha ta yi a Bucha na kasar Ukraine.

Bugu da kari shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yi kira a kori Rasha daga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya yadda ba za ta iya hawa kujerar naki ba akan dukkan wani hukunci da kwamitin zai  zartar akan ta'asar da Rashar ta aikata.

Mutane fiye da miliyan goma sha daya suka tagaiyara tun bayan da Rasha ta kaiwa Ukraine mamaya a ranar 24 ga watan Fabrairu.
 


News Source:   DW (dw.com)