Moussa Faki na neman a kai zuciya nesa a El-Fasher na Sudan

Cikin wata sanarwa da ya fitar a cibiyar Au da ke birnin Addis Ababa, shugaban hukumarr zartaswa na Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya yi kakkausar suka kan yadda rikicin Sudan ke kara ta'azzara da kuma yaduwa, kuma ya yi kira ga kwamitin sulhu da tsaro na AU da ya duba lamarin cikin gaggawa.

Karin bayani: Zaman sulhu ya kasa magance rikicin da Sudan ke fama da shi

Dama dai makomar El-Fasher mai mutane miliyan biyu ta dade tana damun kasashen duniya, saboda ya kasance babban birnin daya tilo na Jihohi biyar na yankin Darfur da bai kasance a karkashin dakarun hannun RSF ba, wadanda ke fafatawa da sojojin gwamnatin Sudan tun Afrilun 2023. Ana zargin bangarorin biyu da aikata laifukan yaki da suka hada da kai hari kan fararen hula, da yin luguden wuta na ba gaira ba dalili, da wawashe muhimman kayayyakin jin kai.

 


News Source:   DW (dw.com)