Motocin sun shiga Gaza ne ta mashigin Rafah da ke kan iyaka da Masar inda daga nan aka yi musu jagora ta mashigin Kerem Shalom ta tsallaken iyakar Isra'ila domin hukumomin su bincika tare da bayar da sahalewar su wuce zuwa Gaza.
Daga cikin motocin da suka shiga Gaza sun hada da tankokin mai 25 kamar yadda wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa.
Tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki a ranar lahadi manyan motocin kayan agaji fiye da 1,700 suka tsallaka daga Masar zuwa zirin Gaza a cewar wakilai. Akwai kuma karin motoci kimanin 4000 da suke jiran shiga yankin na Gaza.