A watan Oktoban 2023, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da bada tallafin karin Euro miliyan 60 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 65.4 domin shigar da kayan agajin jinkai da suka hadar da ruwa da abinci da magunguna ga dubban 'yan gudun hijra da ke jibge a sassa daban daban na Lebanon.
Karin bayani: Jamus za ta bai wa Lebanon tallafin Euro miliyan 60
Ministar ta shaida wa Firaministan Lebanon Najib Mikati cewa Jamus ta damu matuka kan halin da ake ciki a Lebanon kamar yadda kasar ke fadi tashin wanzar da zaman lafiya.
Karin bayani: Hezbollah ta ci alwashin daukar fansa kan Israila
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa mutane sama da 800,000 na tsananin bukatar agajin jinkai. Kazalika, akwai kimanin 'yan gudun hijrar kasar Siriya da ke jibge a Lebanon kimanin miliyan 1.2 wadanda yaki ya raba su da kasar su ta asali.