Goran Vesic ya ce zai yi murabus ne domin ya zama misali ga wasu, sakamakon hatsarin ya faru ne a karkashin sashin da ya ke jagoranta. Sai dai kuma ministan bai amince da daukar alhakin mutuwar mutane 14 din ba da suka gamu da ajalinsu a ranar Juma'ar da ta gabata.
Wannan mumunan hatsarin dai ya haifar da cecekuce a kasar ta Serbia, inda mutane suka rika Allah wadai da jami'an gwamnatin kasar, da kuma nuna takaicinsu kan abun da suka zarga da rashin sanya ido da samar da gine-gine marasa inganci. Mai gabatar da kara na Novi Sad ya ce ana gudanar da bincike kan hatsari.