Sama da al'ummar Najeriya miliyan 33 ne ke fuskantar barazanar yunwa a shekarar da ke tafe ta 2025.
A cewar wani rahoton gwamnatin kasar hadin gwiwa da na wasu hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin sa-kai, matsalar tsaro da ta sauyin yanayi gami da hauhawar farashin kayayyakin abinci na taka muhimmiyar rawa.
A cewar rahoton jihohi kasar 26 musamman wadanda ke arewaci da tsakiyar kasar ne ke a cikin wannan hadari.
Yanzu haka mutane sama da miliyan 25 ne ke fama da matsalar karancin abinci a kasar da ke da yawan al'umma sama da miliyan 200.
Karin BayaniTsadar rayuwa a arewacin Najeriya: