Ziyarar da ta fara a yau Litinin za ta je har yankin Xinjiang, inda za ta tattauna da mutanen yankin domin duba zarge-zargen da ake yi wa mahukuntan kasar na cin zarafin mutane musamman 'yan kabilar Wiga da ake zargin sama da mutane miliyan guda ne ake tsare da su a wani sansani.
Tun a shekarar 2018 hukumar ta bukaci izinin kai ziyara yankin na Xinjiang, wanda sai a wannan karan mahukuntan na Sin suka amince.
Gabannin fara wannan ziyara Amirka da ke zaman doya da manja da China ta nuna damuwarta a kan abin da ta ce shugabar hukumar da wuya ta yi nasarar a binciken da za ta gudanar a kasar, kasancewar mahukuntan na Beijing sun sha musanta zargin cin zarafin al'ummar kasarta..