Merz ya gayyaci Netenyahu Jamus don yaukaka diflomasiyya

Netanyahun ne dai ya sanar da goron gayyatar a wata sanarwa da ofishin Firaministan ya fitar, inda ya ce yana fatan kulla kyakkyawar alaka da sabon Shugaban Gwamnatin Jamus mai jiran gado kuma Jagoran jam'iyyar 'yan mazan jiya kuma wanda ya lashe zaben da aka gudanar a Jamus Friedrich Merz.

Karin bayani: Merkel ta soki Merz kan hadin kai da AfD 

Mr. Merz ya sanar da shugabannin jam'iyyarsa ta CDU cewa ya tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho inda kuma ya bukaci ganawarsu cikin gaggawa da zarar an tabbatar da shi a matsayin Shugaban Gwamnati, ya kuma kara da cewa zai bi dukkan hanyoyin da ya dace domin zuwan Firaministan ba tare da ya fuskanci tirjaya ba.

Karin bayani: An tafka muhawarar kashe kafin babban zaben Jamus

A bara ne dai Kotun ICC ta bada sammacin cafke Netanyahu da kuma tsohon ministan tsaro na Isra'ila Yoav Gallant sakamakon hannu da suke da shi a yakin Gaza wanda ya yi sanadiyyar dubban rayuka na fararen hula.

 

 


News Source:   DW (dw.com)