Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana yadda dangantakarta ta kasance tsakaninta da shugabannin duniya kamar shugaban Rasha Vladimir Putin da Donald Trump a zamanin mulkinta na shekaru 16 a littafin da ta rubuta na waiwayen baya yayin da ta ke shan suka cewa ita ce ummul haba'isin rikicin da ake fama da shi a yanzu.
Merkel yayin da ta ke jawabi a Berlin a bikin cikar ta shekaru 70 da haihuwaHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture allianceA ta'alikin da aka fitar gabanin kaddamar da littafin wanda za a yi a ranar 26 ga watan Nuwamba, Merkel ta tabbatar da kudirinta na kin amincewa Ukraine zama mamba a kungiyar kawancen tsaro ta NATO a taron kolin kungiyar da aka yi a 2008 a Bucharest wanda manazarta suka ce mai yiwuwa hakan shi ya hana Rasha kai wa Ukraine mamaya a wancan lokaci.
Angela Merkel da Donald TrumpHoto: picture-alliance/AP Photo/E. VucciLittafin na tarihin Merkel ya kuma nuna yadda ta nemi bai wa Paparoma shawara kan yadda zai yi mu'amala da Trump lokacin da aka zabe shi karon farko a matsayin shugaban Amurka, inda ta yi fatan shawo kan mutumin da ta lura yana da halayyar ya samu ko kuma a fasa kowa ya rasa, tare da kokarin jan hankalinsa ka da ya janye daga yarjejeniyar sauyin muhalli da aka cimma a Paris.