Merkel ta soki Merz kan hadin kai da AfD

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki Jam'iyyarta ta Christian Democrats CDU mai matsakaicin ra'ayi da yin amfani da goyon bayan jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki a Jamus wajen gabatar da tsattsauran kudiri kan bakin haure a majalisar dokoki.

Merkel ta ce shugaban Jam'iyyar Friedrich Merz ya fada a watan Nuwamba cewa ba zai dauki makamancin wannan mataki ba tare da hadin kai da Jam'iyyar AfD kafin zaben da ake shirin gudanarwa a ranar 23 ga watan Fabrairu ba. Ta na mai cewa wannan ko kadan bai dace ba.

Jawabin nata na zuwa ne bayan da Merz ya kada kuri'a kan kudirin da ke bukatar Jamus ta mayar da bakin haure da suka nemi shigowa kan iyakarta.

Ba kasafai dai Merkel ke tsoma baki cikin al'amura ba tun bayan da ta sauka daga karagar mulki.

 


News Source:   DW (dw.com)